Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini

FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar AddiniKodayake ban sani ba ko ka taba yin karatun aikin Jarida ko kuma yin aiki a wata kafar yada labarai ba kafin zuwanka tashar Talabijin ta Arewa24 kana gabatar da Shirin Kudin Kannywood.Amma katobar tambaya don neman suna da cewa ka kware da sakin baki ya hambarar da kai ga yin tambaya game da Addinin Allah a wajen da ba muhallinsa ba tunda shirin nishadi ne a cikin kayanka na sanyi ga Jaruma Umma Shehu.

Wauta da rashin sanin makamar kwadagonka sun sanya ka yin shirme ga Addinin da ba ka isa ka bata ba ko ita Umma ta bata ba.Na daya Addinni ya kyamaci kure don tozarci,kamar yadda ya shimfida ka’idar kare mutuncin Musulmi(Momoh a duba Arba’unan Nawwawi)!Ina fada maka ne don ka mai da maganar nishadi ta Addini alhali babu kira bai kamata mu ga gawayi ba,ballantana abin da ya ci shi!

Ga wasu ‘Yan tambayoyi don Allah.Ko meye burgewa idan ka bayyanawa Musulmai da wadanda ba Musulmai ba cewa wani Musulmi bai fahimci komai a cikin Addininsa ba?
Ko a tunaninka gyara ne don gaba ko kure ne da tozarci ka yi?
Ko a matsayin ka na Dan Fim nasara ce idan ka wulakanta Abokiyar Sana’arka da ta fiddo ka tare da yi maka Riga da Wando?
A matsayin na Babban mai gabatar wa ko me ka jawo wa wurin aikinku da irin wannan shibircin aikin da bai kai ko da darajar ruwan Aski ba?
A ganinka yadda kake hira da su da irin wannan salon kana dariya,nan gaba da bayyanar haka wasu za su ci gaba da halartar shirin naka,to ci gaba ko aikin mai ginin rijiya?
Da a ce kokarinka na mai kwazo ne a harkar Addini da bakinka bai sanya ka bar shirin ya fita ba tunda za a Iya tace shi!
An ta jin Hujjojin buge na cewa ita ta tado maganar to kai aikin me kake yi a matsayin(anchor) watau Madugun gabatarwa?Kai sai ka zama rakumi marar akala bayan ka yi takalarka!
Zai kyautu hukumomin tashar su taka maka birkin karfe don ka San me za ka rika fada lura da sukar da tashar ke Sha kan bata tarbiyya daga wadanda ke caccaka!
Bai kamaci mai hankali ya Yanke mata hukunci da cin mutuncinka ba lura da ba-zata,kamar kuma yadda ya kamata kowa ya fahimci cewa ka nufi daji.
Amma tunda da Addini ka ke,to ka zo da wuta mai shi na da ruwa!

©Comr.Kabir Sa’idu Bahaushe
08038387516

FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Manazarta al'amuran yau da gobe musammam wanda suka kware a aikin jarida sun fadi ra'ayoyin
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta kunyata a idon duniya a
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
A wata fira da gogagge kuma jajirtaccen jarumin wasannin fina-finan Hausa na Kannywood watau Aminu
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Shahararre kuma tsohon jarumin wasan Hausa fim Aminu Sharif wanda aka fi sani da Momoh
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
"Yadda nayi soyayya da kanwata a film"- Ramadan Booth Jarumin fina-finan Hausa, Ramadan Booth, ya
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Korarriyar Jarumar Finafinan Hausa Rahama Sadau ta fito fili karara ta nuna nadamar rungumar da
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Batun lalata da yan matan a Kannywood ya abu ne daya dade ana tattaunawa, inda
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Fitacciyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta fada
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Jaruma Nafisat Abdullahi ta aika sako ga yan sa ido a shafin ta na Instagram.
FB_IMG_1507589848626 Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Sharif Momo Abisa Kure Da Yayiwa Jaruma Umma Shehu Akan Maganar Addini
Labaran da muke samu daga majiyoyin mu masu karfi da nagarta na nuna mana cewa

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close