Category: news

News: ‘Yan majalisar Nigeria sun sayi motocin ‘kece-raini’ 200 Yayin Da Talakawa Suke Fama Da Abinda Zasu ci

‘Yan majalisar wakilan Najeriya sun saya wa kansu motoci na alfarma 200 kirar fijo 508 daga kamfanin kera fijo na kasar, Peugeot Automobile Nigeria Limited. Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Mr. Abdulrazak Namdas, ya shaida wa BBC cewa an sayi motocin ne domin ‘yan majalisar su samu damar gudanar da ayyukan kwamitoci da kyau.

Yanzu Yanzu: Majalisa Taba Da Umurnin Kamo Shugaban Kamfanin Sadarwa Ta Glo, Dama Wasu Manyan Mutane 30 (Kalli Jerin Sunayen)

A ranar Juma’a 4 ga watan Agusta, majalisar dattawa ba yan sanda umurnin kama shugabannin kamfanoni 30 da ake zargin su da hannu cikin zambar kudaden shiga. Kamfanoni 63 aka zarga da hannu a cikin zambar kudaden shiga na kimanin naira triliyan 30 sannan kuma majalisar dattawa ta gayyace su amma 33 ne kadai suka
Close