Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi

vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu DatayiFitacciyar jaruma ‘yar wasan Hausa mai suna Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta nemi yafiyarmasarautar Kano a bisa rike tagwayen masu da ta yi a cikin wani sabon fim da ake kan dauka a yanzu mai suna ‘Dan Tijara’.

Tagwayen masu dai ababe ne guda biyu masu launin kore da ja da sarakunan Kano ke amfani da su tun kafin zuwan Fulani, wanda ya samo asali tun zamanin wasu tagwaye sarakunan Kano da suka yi mulki a lokaci guda.

A cewar Daso bata taba tunanin cewa rike tagwayen masu zai zamo sabawa ga masarautar ba.

Ta bayyana cewa ta dauki hoto da masun ne sakamakon sha’awa da suke bata, kuma duba da cewa ba na ainihi ba ne, kamar yadda Nasir Zango ya rahoto a shafinsa na Facebook.

A cikin fim din na ‘Dan Tijara’, jarumi Ali Nuhu ne ya fito a matsayin sarki inda ya yi ta sanya kayan sarauta na alfarma, har ma kuma ya rike tagwayen masun.

Yayin da ake daukan fim din ne wasu daga cikin jarumai mata kamar su Halima Atete, Mai Gado da ita Saratu Gidado suka yanke hukuncin daukan hoto da Tagwayen masun, lamarin da ya zame masu laifi.

Wata majiya daga fadar sarkin Kano ta ce rike wadanan masu ga wani sabawa dokar masarautar Kano ne domin anyita ne don sarki kadai.

Harma ta kara da cewa akwai wani zamani da wani sarki a masarautar Jigawa ya so mallakar masun ammamasarautar Kano ta taka masa birki.

Daso dai ta ce ta tuba a yafe mata da laifin da aka ce ta aikata.

vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Fitaccen jarumin nan, mai bayar da umurni, mai shiryawa da kuma koyar da rawa a
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Sunayen sabbin jarumai 5 dake tashe a dandalin kannywood a halin yanzu ciki har da
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Batun lalata da yan matan a Kannywood ya abu ne daya dade ana tattaunawa, inda
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Jaruma Nafisat Abdullahi ta aika sako ga yan sa ido a shafin ta na Instagram.
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Labaran da muke samu daga majiyoyin mu masu karfi da nagarta na nuna mana cewa
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Manazarta al'amuran yau da gobe musammam wanda suka kware a aikin jarida sun fadi ra'ayoyin
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Tsakure a cikin wata tattaunawa da Aminu Shariff Momo ya yi da sabuwar Jarumar Finafinan
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Jarumi General BMB na daya daga cikin mutanen da basu ji dadin tambayar da Aminu
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Labaran da muke samu yanzu ba da dadewawa ba nan nuni da cewa fitacciyar jarumar
vllkyt36eqv5omumu.4a7c6bd5 Daso Ta Nemi Afuwar Masaurautar Kano Game Da Rike Tagwayen Masu Datayi
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta kunyata a idon duniya a

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close