Kannywood: ‘Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne’ – Sadik Sani Sadik

2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik

Fitaccen jarumin Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce kwarewarsa ta iya taka kowacce rawa ce ta sa ya lashe gasar jarumin jarumai sau uku a jere.

“Idan har Ina cikin Kannywood ni ne zan ci gaba da lashe gasar jarumin jarumai a ko wacce shekara saboda ba na wasa da aikina”, in ji Sadiq Sani Sadiq, a tattaunawa ta musamman da BBC Hausa.

Ya musanta zargin da ake yi cewa yana jajircewa a fim ne domin ya dusashe taurarin jarumai Ali Nuhu da Adam Zango, yana mai cewa “su iyayen gidana ne domin kuwa sun taimaka min sosai a wannan harkar. Ka ga kuwa babu wanda zai ja da iyayen dakinsa.”

A cewarsa, “Ni ina yin fim ne a matsayina na Sadiq Sani Sadiq, kuma ina da kwazo, da jajircewa, da mayar da hankali sosai a kan aikina, shi ya sa nake ganin babu wata gasa da za a yi da ba zan lashe ba.”

Sadiq Sani Sadiq, wanda ake yi wa lakabi da Dan marayan zaki, ya kara da cewa yana son dansa ya gaje shi.

2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani SadikSadiq ya ce ya kamata a rika yi wa ‘yan fim uzuri

Jarumin ya ce a baya ya yi kiwon karnuka sosai shi ya sa “da aka sa ni a wani fim a matsayin mafarauci ban fuskanci wata matsala ba”.

“Abin da ya sa nake iya taka ko wacce rawa shi ne, na yi hulda da mutane daban-daban a rayuwa tun ma kafin na soma fim. Shi ya sa idan aka sa ni a matsayin mai sayar da shayi, misali, za ka ga na yi abin tamkar mai shayin gaske saboda na taba yin hulda da shi,” in ji jarumin.

Sadiq Sani Sadiq ya bayyana zargin da ake yi wa ‘yan fim na neman maza da cewa “karya ce kawai. Ni ban taba ji ko ganin wanda yake luwadi ba. Kuma na dade Ina yin fim. Ka ga kuwa tun da haka ne sai kawai in ce karya da kazafi ake yi mana.”

Ya ce ba aikin ‘yan fim ne koyar da mutane tarbiya ba kamar yadda wasu ke hasashe, yana mai cewa, “duk wanda ya ce ‘yan fim sun bata masa tarbiyya da ma ba shi da ita. Ai tun daga gida ake samun tarbiyya”.

2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Musha Dariya Tareda Jarumi Kuma Mai Bada Dariya Wato Sadik Sani Sadik Cikin Wani Sabon
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Fitaccen jarumin nan na wasan fina-finan Hausa mai suna Sadiq Sani Sadiq da wasu ke
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Fitaccen jarumin finafinan Hausa nan ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya yi bikin sunan jaririyar
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Sani Sadiq ya kasance shaharen dan wasan fim din Hausa, daya daga cikin jaruman da
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Labarin da muke samu yana nuna mana da cewa fitaccen jarumin wasannin fina-finan Hausa na
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Labaran da muke samu daga majiyoyin mu masu karfi da nagarta na nuna mana cewa
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Manazarta al'amuran yau da gobe musammam wanda suka kware a aikin jarida sun fadi ra'ayoyin
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Tsakure a cikin wata tattaunawa da Aminu Shariff Momo ya yi da sabuwar Jarumar Finafinan
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Jarumi General BMB na daya daga cikin mutanen da basu ji dadin tambayar da Aminu
2016-09-16--06_09_42 Kannywood: 'Ali Nuhu da Adam Zango iyayen gidana ne' - Sadik Sani Sadik
Labaran da muke samu yanzu ba da dadewawa ba nan nuni da cewa fitacciyar jarumar

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close