Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe

C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo KarsheDa alama dai rikicin da ake ta yayatawa dake tsakanin manya kuma shahararrun jaruman nan mata na masana’antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe komai ya wuce.

Mun dai fahimci hakan ne ta dalilin wani rubutu da jaruma Rahma Sadau tayi a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook inda take taya abokiyar sana’ar tata watau Nafisa Abdullahi murna dangane da wani muhimmin ci gaba da ta samu.

HausaTop.com dai ta samu cewa Rahma Sadau din ta yada labarin ne da jaridar nan ta Pulse Nigeriya Hausa ta wallafa mai taken ‘Nafisa Abdullahi: Jaruma ta zama jkada’ inda ta rubuta ‘Congrats sis’ a harshen turanci da ke nufin ‘ina taya ki murna ‘yar uwa’ da Hausa.

A kwanan baya ne dai cikin watan Afrilu kungiyar mashirya fina finai na Kannywood suka shiga tsakanin jaruman yan fim din nan su biyu Nafisa Abdullahi da Hadiza Gabon bayan wata arkalla data shiga tsakaninsu.

Shaidan dai ya shiga tsakanin jarumai matan ne a jihar Kaduna yayin da suke bakin aiki wajen shirya wani fim a garin na Kaduna, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Korarriyar Jarumar Finafinan Hausa Rahama Sadau ta fito fili karara ta nuna nadamar rungumar da
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Korarriyar jarumar finafinan Hausa da aka kora ta koma yin finafinan Turanci na kudancin kasar
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Idan baku mantaba ClassiQ Dai shine mawakain da ya gayyaceta a wani videon wakar sa
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Farawa da iyawa fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da a
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Kamar Yadda Kowa Yasani Jaruma Rahama Sadau Bata Dauki Saka Kananun Kaya Da Barin Gashi
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu na nuni da cewa masana'antar Kannywood na
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Jaruma Rahama Sadau Dai Kullum Kara Nisa Take A Fina Finan Nollywood Ku Kalli Wannan
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina finan Hausa wadda kuma yanzu haka ke a matsayin
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Kamar Yadda Kuka Sani Akwai Takun Saka Tsakanin Manyan Jaruman Nan Guda Wato Nafisa Abdullahi
C-BrwVvUQAEy0IE Kannywood: Da Alama Rikicin Rahma Sadau Da Nafisa Abdullahi Yazo Karshe
Shan koko kwanciyar rai, inji bahaushe, kuma dama ai so hana ganin laifi. Irin haka

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close