Nafi Buhari Bawa ‘yan Nigeria ‘yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mayar da martani ga yunkurin gwamnatin kasar na yin dokar da ta haramta furta kalaman nuna kiyayya tsakanin al’ummomin kasar.

Mista Jonathan ya sake wallafa wani hoto a shafinsa na Facebook wanda ya yake dauke da rubutu kamar haka:

“Ni ne shugaban da aka fi zagi da suka a duniya, amma za a tuna da ni idan na bar mulki saboda cikakken ‘yancin da gwamnatina ta bai wa jama’a,” kamar yadda sakon ya ce.

Ya wallafa wannan sakon ne a shafin ranar Alhamis bayan wallafawar farko a watan Disambar shekarar shekarar 2014.

A makon jiya ne Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya ce gwamnati za ta fara daukar amfani da kalaman nuna kiyayya a matsayin ta’addanci.

Hakazalika a jawabin da Shugaba Buhari ya yi wa al’ummar kasar ranar Litinin, ya tabo batun yadda wasu suke kalaman da suke ketara ikokin dokokin kasar a kafofin sada zumunta.

Abin da ya sa wasu ‘yan kasar suke ganin wata kila gwamnati ba ta jin dadin yadda jama’a suke sukarta musamman a kafofin sadarwa na zamani.

A ranar 12 ga watan Agustan nan ne gwamnatin Najeriyar ta ce ta fara shirye-shiryen aike wa da wata bukata zuwa ga majalisar dokokin kasar da ke neman yin dokar da za ta fayyace irin hukuncin da za a yi kan wadanda aka samu suna furta kalaman kiyayya ga wani jinsi a kasar.

Gwamnati ta yanke shawarar yin hakan ne saboda yadda zaman tankiya ke karuwa tsakanin a kabilu da addinai da kuma yankunan kasar daban-daban, inda har wasu ke kiran da a raba ta ko a sake mata fasali.

_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Wani dan Najeriya mai suna Johnny Creed yana neman shawarar 'yan Najeriya bayan da ya
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Shugaba Muhammad Buhari ya isa Babban birnin tarayya Abuja a yau Laraba bayan kammala hutun
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Ba baskiya bane cewar wai shugaba Muhammadu Buhari ya shirya tsaf zuwa kasar Amurka bisa
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Kungiyar nan da ke kiran kansu ta yan uwa musulmai mabiya tafarkin shi'a a Najeriya
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane biyu dangane da kisan wani soja, Las
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya shirya don komawa gida Nijeriya bayan tabbatar da samun
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Wannan bawan Allah da kuke gani, sakataren wani Coci ne a cikin wani kauye dake
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Honarabul Gudaji Kazaure ya bayyana cewa asiri aka yi
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
A Nigeria, ga alamu kokarin da hukumomin kasar ke yi na fadada yaki da cin
_97536547_457046285 Nafi Buhari Bawa 'yan Nigeria 'yanci — Inji Tsohon Shugaban Kasa Jonathan
Bincike ya nuna cewa jami'an tsaro sun kama shahararren marubucin nan da ya saba fashin

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close