Nayi Murnar Mutuwar Wannan Yaro (LIL AMEER) Matuka – Inji Mal. Shuaibu Salih Zaria

 

_97819834_mediaitem97813503 Nayi Murnar Mutuwar Wannan Yaro (LIL AMEER) Matuka - Inji Mal. Shuaibu Salih ZariaA lokacin da naga Duniyar Social Media ta dau dumin bada labarin mutuwar wannan yaro, nan take na fara bincike kan rayuwar sa.

Abinda bincikena ya tabbatar min shine: Wannan yaro mawaki ne wanda ake mishi take da ‘Dan Autan Mawaka.

Nayi takaici matuka da naga wannan bayani, ace yaron da alama ke nuna bai balaga ba, dan musulmai a Arewacin Nigeria ya zama mawaki irin mawakan turawa har ya shahara a duniya, wallahi wannan abun bakin ciki ne ga al’ummarmu. Domin inada tabbas da yayi tsawon rayuwa, to da yayi rayuwa mara anfani ga al’umma.

Amma da yake Allah Ra’ufur Rahim ne sai ya dauki rayuwarsa tun gabanin ya balaga, gabanin shari’a ta hau kan sa.

Ina rokon Allah ya gafarta masa yasa Aljannah makomarsa da mu baki daya. Allah ka tsare mana zuriyarmu daga tanbadewa Ameen.

_97819834_mediaitem97813503 Nayi Murnar Mutuwar Wannan Yaro (LIL AMEER) Matuka - Inji Mal. Shuaibu Salih Zaria
Idan idi ya kasance a ranar Juma'a to babu wajibcin sallar Juma'a a ranar; wannan

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close