NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama

B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin SamaSakamakon matakan da babban Bankin Najeriya CBN ke dauka na ‘kara sayar da takardar kudin Dalar Amurka ga bankuna da ‘yan canji, yanzu haka darajar Naira na sama na ‘kasa.
WASHINGTON D.C. – —

Duk da Miliyoyin Dalar Amurka da Babban Bankin Najeriya ke fitarwa ga bankunan ‘yan kasuwa da kuma masu hada-hadar kudaden kasashen ketare duk mako, har yanzu farashin Dalar Amurka na ci gaba da hawa kan kudin Naira, ko da yake a baya an samu karyewar kudin na Dala.

Alhaji Bello Datti, masanin tattalin arziki da hada-hadar kudaden ketare da ke Legas, ya ce dalilin da yasa farashin Dala yake sama yana ‘kasa shine saboda yanayin masu karbar kaya, kasancewar rana ‘daya kamfanoni da mutane zasu zo neman sayar kudin Dala wanda idan masu nemanta suka yi yawa, farashinta kan yi sama. Wasu lokuta kuma idan babu masu neman sayan Dala farashinta kan yi ‘kasa ne.

Sai kuma a cewar babban bankin Najeriya, ya dauki matakin ‘kara yawan Dalolin da ya ke bayarwa musamman ga masu fita kasashen ketare da rijistar makarantu da masu zuwa a duba lafiyarsu da kuma wasu kayayyakin kasuwanci da ba a haramta shigowa da su ba.

Duk da wannan mataki da babban bankin yake ‘dauka masu masana’antu a Najeriya na ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Yayin da masana tattalin arziki da sauran ‘yan Najeriya ke ci gaba da yin nazari game da matakin na CBN, na ‘kara adadin yawan kudaden Dalar Amurka a cikin gida. A waje ‘daya kuma fatan gwamnati shine na ‘kara yawan kudaden da ta ke samu daga cinikin Man Fetur wanda ya karye a kasuwannin duniya.

Daga: voahausa

B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari tab a da tsokaci kan samun lafiyar shugaban kasa
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
Zan Kamo Jonathan, A Yammacin Yau. Shugaban hukumar EFCC, a Najeriya, Ibrahim Magu, ya yi
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
A cikin yukurin su na dakile yada labaran karya marasa tushe, kamfanin zumunta na yanar
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
*Masari Ya Sha Ruwan Duwatsu. Sanata ABU IBRAHIM mai wakiltar yankin FUNTUWA ya sha mugun
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
Akwai maganganu daga majiya mai karfi kan cewar fitaccen dan wasan kwallon nan na kulob(club)
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
 Jita-jita tayi yawa akan cewa sojoji sunyi wa Sani Danja dukan tsiya. Wanda har a
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
Mawakin Nura M Inuwa Yana Gayyatar Kowa Da Kowa Zuwa Wajan Daurin Aurensa  Ga Katin
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
Dama rai da jini dole ya zamo suna samin tangarda yau da lafiya wata rana
B6B77558-A433-4B1E-81C5-27A994B72AB4_cx0_cy10_cw0_w408_r1_s NEWS: Darajar Naira Tana Kara Yin Sama
Bayan sabuwar wakar sa ta ‘Kano ta Ganduje ce’, an kona gidan mawaki RararaFitaccen mawakin siyasar

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close