Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam’iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??

APC-logo Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam'iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??Tun bayan kammala zabubbukan shekara ta 2015 wanda yabawa jam’iyyar APC nasara sai rikice-rikicen cikin gida suka dabaibaye Jam’iyyar tun daga mataki na kasa har zuwa jihohi da kananan hukumomi, masu fashin baki a harkokin siyasa na fassara wannan rikice-rikice ta sigogi daban-daban

Koma dai menene yana da kyau shugabannin wannan jam’iyya mai farin jini su tsaya kai da fata wajen ganin an samu saukin wannan rikice-rikice musamman a Jihohi inda nan ne wannan lamari ya fi ta’azzara, domin yau kusan shekaru biyu kenan ana tafka wannan hatsaniya a cikin jam’iyyar ta APC amma sun kame bakinsu sunyi Gum wanda hakan yake nuna basu da niyyar kawo daidaito acikin wannan jam’iyya hakan kuma alama ce dake nunawa cewar basa bukatar APCN ta sake cin zabe a shekara ta 2019 mai zuwa

Muna so mu fadawa wancan shugabanni cewar ya zama wajibi agaresu muddin suna amsa sunayensu na shugabannin APC a kasa to su kawo karshen Zaman Doya da Manja da akeyi tsakanin Gwamna Mallam Nasiru elrufa’i na jihar Kaduna da Sanata Shehu Sani, ya kuma zame musu Tilas su daidaita tsakanin Sanata Danjuma Goje da Sanata Bayero Nafada, su yi kokari su ga sun dakile balahirar dake karuwa tsakanin ‘yan Majalisar tarayya na jihar Bauchi da Gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubaka, matukar muna so mu ci zabe a APC to dole ne a kashe wutar rikicin da kullum wasu ke watsa mata fetur a jihar Kano tsakanin magoya bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Wannan kusan sune manya-manyan waki’oin da suka afkawa jam’iyyarmu ta APC idan ka cire wawakeken gibi da aka samu tsakanin Gwamnatin Tarayya da majalisun dokokin kasar nan domin nan ma wata tsumammiyar Rigima ce ke cigaba da tsuma kuma na Tabbata da zarar shugaban kasa ya dawo za’a ci gaba da inda aka tsaya akan wannan Rigima, saboda haka mu kirane kawai Garemu zuwa garesu su shugabbanin jam’iyya idan sunji sun gyara shike nan idan kuma sun ki gyarawa shike nan

Idan kunne yaji to jiki ya tsira!!!

APC-logo Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam'iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??
Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Rashida Adamu Abdullahi wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa'a
APC-logo Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam'iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??
ya kuma zargi gwamnatin Kano da daukar nauyin masu yada jita-jitar komawarsa PDP Tsohon gwamnan
APC-logo Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam'iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??
Jami'an tsaro a Jihar Sakkwato sun dakatar da mabiyan akidar Kwankwasiyya gudanar da taro ba
APC-logo Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam'iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??
Shahararren Mawakin Siyasa Wato Dauda Kahutu Rara Yashaida Mana Cewa Akwai Babban Tanadi Dayayiwa Masoya
APC-logo Siyasa: Anya Kuwa Shugabannin Jam'iyyar APC Sunaso Ta Sake Cin Zabe??
Jam’iyyar APC ta kasa ta dauki wani mataki da ake ganin raba gardama ne akan
Tags:,

Add a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Close